Hausa Translation:
EFCC Ta Gurfanar Da Mutum Hudu Bayan Ta Tuhume Su Da Baiwa Masu Zabe Cin Hanci
Hukumar EFCC shiyyar Ilorin ranar Litinin, 24 ga watan Oktoba, 2022, ta gurfanar da wasu mutane hudu a gaban mai shari’a Mathias Agboola na babbar kotu dake Oshogbo.
Hukumar EFCC na tuhumar su da baiwa masu kada kuri’a cin hanci lokacin zaben jihar Osun da ya gudana a 16 ga watan Yuli,2022.
Wadanda hukumar EFCC ta gurfanar sune Adeyemo Bahiru Abiodun, Abidogun Ismail, Jimoh Kazeem da Yekini Nurudeen Abiodun
Jami’an hukumar EFCC ne suka kama su a wuraren kada zabe daban bayan sun sami bayanan sirri dake nuna suna bayar da toshiyar baki.
Sun musanta laifin da ake tuhumar su dashi.
Mai shari’ar ya bayar da belin su akan Naira miliyan biyu tare da mai kare su inda ya daga sauraren karar zuwa 21 da 28 ga watan Nuwamba, 2022.